A sanarwar da kwamitin mai mambobi 15 ya fitar ya ce ya lura da irin takun sakar dake wanzuwa tsakanin bangaren shugaban kasa da na firaministan kasar wanda hakan na iya mayar da hannun agogo baya ga cigaban kasar tun bayan dawowar tsarin gwamnati mai bin doka da oda bayan kammala babban zaben kasar a shekarar 2014.
Rahotannin sun bayyana cewar rashin jituwar dake wanzuwa tsakanin bangaren shugaban kasar da firaiministan zai iya jefa kasar cikin tashin hankali.
Kwamitin MDD ya jaddada bukatar bangarorin biyu da su dinke barakar dake tsakaninsu ta hanyar hawa teburin sulhu da gudanar da gwamnati mai tsabta da shimfida tsarin mulki na fararen hula mai cike da 'yanci, ta haka ne kadai kasar za ta samu dawamamman zaman lafiya.
Kazalika kwamitin na MDD ya bayyana muntunta dokokin kasa da kula da hakkin al'ummar kasar na daga cikin abubuwan da za su taimakawa kasar ta Guinea Bissau samun zaman lafiya mai dorewa. (Ahmad)