A jiya Jumma'a, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin (CPPCC) Yu Zhengsheng ya gana da shugabar majalisar tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta Guinea madam Haja Rabiyatu Serra Diallo a birnin Beijing.
Yu Zhengsheng ya bayyana cewa, a cikin shekaru 57 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Guinea, an kara samun amincewar juna a fannin siyasa, kasashen biyu suna nunawa juna goyon baya kan batutuwan da suka shafi babbar moriyar juna, da harkokin da suka fi jawo hankulansu, tare da samun sakamako mai kyau wajen yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, da cinikayya tsakaninsu. Sin tana dora muhimmanci sosai kan dangantaka tsakaninta da Guinea. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Guinea sun yi fasali bisa manyan tsare tsare kan raya dangantakar dake tsakaninsu. Sin na fatan yin hadin gwiwa tare da Guinea, domin tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa mu'amala tsakaninsu, da zummar kara kawo alheri ga jama'arsu.
A nata bangare, madam Haja Rabiyatu Serra Diallo ta bayyana cewa, akwai dankon zumunci tsakanin Guinea da Sin, ta nuna godiya ga kasar Sin wajen ba da taimako cikin dogon lokaci. Da fatan kasar za ta kara yin musayar ra'ayi da samun darasi daga majalisar CPPCC, domin samun ci gaba tare.
Mataimakin shugaban majalisar CPPCC, kana shugaban majalisar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Sin Du Qinglin ya halarci ganawar. (Fatima)