Wani jami'i mai kula da hulda da kafofin watsa labaru na rudunar sojojin kasar Bangladesh ya tabbatar da hakan ga wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin a jiya Asabar. Jami'in wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce cikin wadanda suka mutu akwai maza 10 da mata 10.
'Yan bindiga 7 ne dai suka kai wannan mummunan hari inda suka kashe 'yan sanda 2 a farkon harin, kafin daga bisani su yi awon gaba da wasu 'yan kasashen waje. Sai dai tuni jami'an tsaron kasar Bangladesh suka samu damar kubutar da mutanen 13 da aka yi garkuwa da su a wannan harin.(Bello Wang)




