in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai a Dhaka
2016-07-03 12:50:20 cri
Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon a jiya Asabar ya bayar da sanarwa ta bakin kakakinsa, inda ya yi tur da harin ta'addanci da aka kai a wani dakin cin abinci dake birnin Dhaka, babban birnin kasar Bangladesh.

A cikin sanarwar, Ban Ki-Moon ya nuna juyayi ga iyalan mutanen da suka rasu sakamakon lamarin, da gwamnatin Bangladesh da jama'arta, ya kuma bayyana fatansa na samu sauki ga wadanda suka samu raunuka sakamakon harin.

Ban, ya jadadda cewa, akwai bukatar kasashen duniya da na shiyyar su kara kokari, wajen yaki da ta'addanci yadda ya kamata. Kana ya bayyana cewa, MDD tana cigaba da nuna goyon baya ga gwamnatin Bangladesh kan kokarinta na dakile muggan laifuka.

A wannan rana kuma, kwamitin sulhun MDD shi ma ya bayar da wata sanarwa, inda ya yi Allah wadai da wannan harin ta'addanci da ya afku a Dhaka, ya kuma yi kira da a gurfanar da wadanda ke da hannu a wannan hari a gaban kotu.

Rohotanni sun bayyana cewa, a daren ranar 1 ga wannan watan, wasu dakaru dauke da makamai sun yi garkuwa da wasu mutane a wani dakin cin abinci dake birnin Dhaka. Sakamakon bata kashi tsakanin maharan da jami'an tsaro, lamarin ya yi sanaddiyar rasuwar mutanen 20 da aka yi garkuwa da su, yayin da wasu sama da 40 suka jikkata. Kungiyar mai tsattsauran ra'ayi ta IS ta dauki nauyin kaddamar da harin, amma bangaren 'yan sandan Bangladesh bai tabbatar da hakan ba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China