
Mutane 20 sun mutu a lokacin da wasu mahara dauke da makamai suka farma wani gidan cin abincin Spain dake birnin Dacca na Bangladesh, in ji wani kakakin rundunar sojojin Bangladesh a yayin wani taron manema labarai a ranar Asabar.

Mutane 13 da aka yi garkuwa dasu, wadanda suka hada dan kasar Japan guda, da 'yan kasar Sri-Lanka biyu, an samu ceto bayan samamen da jami'an tsaro suka kai da ya taimaka wajen kawo karshen garkuwa da mutane tun ranar Jumma'a da yamma, tare da kashe maharan shida da cafke wani guda, in ji kakakin. (Maman Ada)




