Alkaluman baya-bayan game da rahoto kan makomar tattalin arzikin duniya, ya nuna faduwar farashin kayayyaki, mummunan yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki da matsalar fari da ta gallabi sassa daban-daban na shiyyar a matsayin dalilan da suka haddasa wannan koma baya.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, ana saran tattalin arzikin kasar Ghana ya bunkasa da kashi 5.2 cikin 100. Wannan kuwa ya samu ne sakamakon yadda kasar ta inganta manufofinta na zuba jari,sabbin filayen mai da kasar ta samu da kuma tabbas da ake da shi kan wutar lantarki na kasar.
Bugu da kari, ana saran tattalin arzikin kasashen Cote d'Ivoire da Kenya za su bunkasa da kashi 8.5 da kuma kashi 5.9 cikin 100 bi da bi, baya ga yadda ake samun ci gaba a harkokin zuba jari da aikin gona na kasashen.,
A cewar rahoton, ana saran tattalin arzikin Najeriya shi ma zai bunkasa da kashi 0.8 cikin 100, wato kasa da kashi 3.8 cikin 100 daga hasashen watan Janairu. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon takunkumin musayar kudaden ketare, karancin mai da raguwar man da kasar ta ke hakowa, lamarin da ya shafi tattalin arzikin kasar nesa ba kusa ba, da kuma tasirin faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.
Sai dai ana ganin tattalin arzikin Afirka ta kudu yana tafiyar hawainiya, inda ya kai kashi 0.6 cikin 100, lamarin da ya haifar da koma bayan harkokin kasuwanci, yayin da rikicin siyasar kasar ya kara rage kuzarin masu sha'awar zuba jari, ga rashin aikin yi da manufofin kudi masu tsauri na kasar sun hana sassa masu zaman kansu gudanar da ayyukansu.(Ibrahim)