Daraktan cibiyar kula da ayyukan gaggawa na kasar Rasha Victor Yatsutsenko, ya tabbatar da mutuwar mutane 62, dake cikin jirgin fasinjan nan da ya yi hadari yana daf da sauka a filin jirgin birnin Rostov-On-Don dake kudancin kasar. Mr. Yatsutsenko ya ce cikin wadanda suka rasu akwai 'yan kasashen waje 12.
Yanzu haka dai an riga an rufe filin jirgin saman na Rostov-On-Don, inda aka fara bincike kan aukuwar hadari. Wasu kwararru sun yi hasashen rashin kyawun yanayi, a matsayin musabbanin aukuwar hadarin. Jihar Rostov ta bayyana gobe Lahadi a matsayin ranar makoki.
Ban da haka kuma, firaministan kasar Sin Li Keqiang da ministan harkokin waje na kasar Wang Yi, sun gabatar da sakon ta'aziyyar su ga gwamnatin kasar Rasha da kuma iyalan mutanen da suka rasa rayukan su.(Lami)