A wannan rana, a cikin shirye-shiryen talebijin mai taken "Zantawa da Putin", shugaban kasar Rasha ya tabo maganar tattalin arzikin kasar a farko, inda ya ce, yanzu, akwai rashin tabbas game da ko da an dakile koma bayan tattalin arzikin kasar, amma abun da za a iya hasashe shi ne, ba za a samu raguwar tattalin arzikin kasar mai tarin yawa ba.
Bugu da kari kuma, Putin ya ce, kasashen Rasha da Amurka sun gudanar da hadin gwiwa cikin armashi game da batun Siriya da yaki da ta'addanci. Putin ya ce, kasashen Rasha da Amurka sun gudanar da aiki cikin hadin gwiwa don shiga tsakani, kuma yana fata za a cimma sakamako mai gamsarwa. Yayin da aka tabo maganar takunkumin da kasashen yammacin duniya suka sanya wa kasarsa, Putin ya yi nuni da cewa, kasashen yammacin duniya ba za su soke takunkumin da suka kakabawa Rasha ba, idan kuma kasashen yammacin duniya ba su soke takunkumi ba, Rasha ita ma za ta ci gaba da hana shigar da kayayyakin abinci na kasashensu.(Bako)