Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya jinjinawa irin ci gaban da nahiyar Afirka ke samu a fannoni da dama, da suka hada da na siyasa, da tattallin arziki.
Mr. Ban ya bayyana hakan ne cikin sakonsa na taya murnar sake zagayowar ranar Afirka ta bana, wadda aka gudanar a ranar Litinin 25 ga watan nan na Mayu. Ya ce, wannan rana ta ba da zarafi na bayyana irin nasarorin da Afirka ta cimma, tare da nazarin irin kalubalen da ke fuskantar nahiyar.
Cikin manyan matsaloli da Afirkan ta fuskanta, a cewar Mr. Ban, akwai batun cutar Ebola wadda ta hallka mutane kusan 11,000 a wasu kasashen yammacin Afirka, tare da jefa al'ummar yankin cikin wahalhalun rayuwa. Sai dai duk da hakan, goyon baya da tallafin da kasashen Afirka, da ma sauran kasashen duniya suka bayar ga wadannan kasashe, sun haifar da nasarar da aka samu ta dakile yaduwar wannan cuta.
Abin da ya rage yanzu haka a ta bakin babban magatakardar MDDr shi ne tabbatar da cutar ba ta sake bulla ba, da aikin sake ginin kasashen da ta yi wa barna, tare da karfafa yanayin zamantakewa, da na gudanarwa a daukacin nahiyar.
Har ila yau Mr. Ban ya yi tsokaci game da muhimmancin bunkasa rayuwar mata, da ba su kariya, da batun cimma muradun Afirka na shekarar 2063, da kuma batun wanzar da zaman lafiya da lumana a nahiyar. (Saminu)