Hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta furta a yau Alhamis a birnin Geneva cewa, an kawo karshen cutar Ebola da ta sake yaduwa daga watan Janairu a kasar Saliyo. Wannan ne karo na biyu da hukumar ta sanar da kawo karshen cutar Ebola a yammacin Afrika.
Hukumar ta WHO ta ce, yau muhimmiyar rana ce ta tinkarar cutar Ebola ta kasar Saliyo, ta jinjina matakan da gwamnatin Saliyo da abokanta da kuma jama'arta suka dauka domin tinkarar cutar.
Hukumar ta WHO ta ce za ta ci gaba da hadin gwiwa tare da kasar Saliyo, domin kafa tsarin kiwon lafiya, ta yadda za ta yi rigakafi da tinkarar ciwace-ciwacen da kasar za ta samu a nan gaba.(Lami)




