in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da dalibai mata dubu biyar da suka yi ciki sun sake komawa makaranta a Saliyo
2016-03-04 10:26:04 cri

Rahotanni daga kasar Saliyo na cewa, sama da dalibai mata dubu 5 da suka yi ciki a lokacin da cutar Ebola ta barke a kasar ne, suka sake komawa makarantun firamare da na sakandare a fadin kasar.

Da yake yiwa manema labarai karin haske game da lamarin mataimakin darektan hulda da jama'a na ma'aikatar ilimi, kimiya da fasahar kere-kere na kasar Brima Turay, ya ce ya gamsu da gwazon daliban da suka koma harkokinsu na karatu.

Jami'in ya ce, gwamnati ce za ta biya kudadensu na karatu na shekaru biyu, yayin da ma'aikatar ilimin kasar tare da hadin gwiwar hukumomin ba da agaji ke shirin tsarawa daliban wasu shirye-shirye da zummar kara karfafa musu gwiwa. Wadannan sun hada da fadada wasu makarantu 377 da a halin yanzu suke da cunkoso, ta yadda ya zuwa shekara 2017, ko wane aji zai kunshi daliban da ba su gaza sama da 45 ba, baya ga shirin ciyar da dalibai da za a bullo da shi.

A shekarar da ta gabata ce ma'aikatar ilimin kasar ta bayar da sanarwar sake baiwa dalibai matan da suka yi ciki damar sake komawa makaranta, don hana sauran daliban da ba su shiga wannan matasla ba yin watsi da harkokinsu na karatu.

Bayanai na nuna cewa, daga bisani dai wannan shiri ya gamu da nakasu, bayan da wasu kungiyoyin kare hakkin bil Adama suka zargi gwamnati da keta hakkin yara mata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China