in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar WHO ta sanar da kawo karshen cutar Ebola a Saliyo
2015-11-08 13:53:04 cri
A ran 7 ga wata, hukumar kiwon lafiyar kasa da kasa ta WHO ta sanar da kawo karshen yaduwar cutar Ebola a kasar Saliyo, wadda ta kasance kasa ta biyu da aka kawo karshen yaduwar cutar a yammacin kasashen Afirka, watau bayan kasar Liberia ta kasance kasa ta farko wajen kawo karshen Ebola.

Sanarwar da hukumar WHO, ta nuna yabo ga gwamnati da jama'ar kasar Saliyo kan babban sakamako da suka samu, bisa kokarin da gwamnatin kasar ta bayar, da kuma hadin gwiwar kasa da kasa, kasar Saliyo ta cimma nasarar yaki da cutar Ebola, kuma za a fara aikin farfadowar kasa yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China