Wasu masana a nahiyar Afirka sun bayyana cewa, shirin zurfafa gyare-gyare da manufofin diflomsiyar kasar Sin za su kai ga inganta tattalin arziki da harkokin masana'antun nahiyar Afirka.
Farfesa Munene Macharia na jami'ar dangantakar kasa da kasa ta Amurka da ke birnin Nairobin Kenya ya ce, wadannan manufofi sun sanya kasar Sin kasancewa kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya cikin dan kankanin lokaci.
Masanin ya ce, yadda kasar ta Sin ta ke ci gaba da mamaye harkokin cinikayyar kasa da kasa, zaman lafiya da tsaro da harkokin da suka shafi muhalli a duniya, na daga cikin abubuwan da ake tattaunawa gabanin tarukan majalisar wakilan jama'ar kasar na NPC da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa wato CPPCC da aka saba gudanarwa a watan Maris.
A nasa bangaren Dr. Gerishon Ikiara na jami'ar Nairobi da ke kasar Kenya, ya ce manyan tarukan kasar na NPC da CPPCC za su kasance masu fa'ida ga nahiyar Afirka, inda ake fatan za su yi bitar dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen na Afirka karkashin dandalin nan na FOCAC.
Dr. Ikiara ya yaba yadda mahukuntan kasar ta Sin ke rungumar matakan yiwa tattalin arzikin kasar gyaran fuska, tsarin da a cewar masanin ya taka muhimmiyar rawa na kasancewar Sin zama kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Masana na ganin cewa, kasar Sin za ta ci gaba da amfani da karfin tattalin arzikinta gami da tasirin da ta ke da shi a harkokin diflomasiya wajen janyo masu sha'awar zuba jari a shirye-shiryen da ake na inganta kayayyakin more rayuwa a kasashen Afirka.(Ibrahim)