Jakadan kasar Sin dake kasar Gabon Sun Jiwen, ya sanar a yayin wata ganawa tare da jami'an diplomisiyya na kasashen Afrika dake kasar Gabon cewa, kasarsa na fatan kara yawan adadin musanyar kasuwanci tare da Afrika daga dalar Amurka biliyan 210 zuwa 400 nan da shekarar 2020.
Kasar Sin za ta kara fafada shigar ta a kasuwannin Afrika, in ji mista Sun Jiwen.
Sin da ta kasance kasar dake kan gaba wajen huldar kasuwanci tare da Afrika tun yau da shekaru shida, kuma tana son kara adadin ciniki daga dalar Amurka biliyan 210 zuwa 400 nan da shekarar 2020, a cewar jami'in.
Haka kuma, ya jaddada cewa, kasarsa na shirin taimakawa kasashen Afrika masu tasowa a cikin shekaru biyar masu zuwa. Kuma manyan ayyukan taimakawa mata da matasa za su kasance a sahun gaba.
Gwamnatin Sin na mai da hankali wajen gina manyan ayyukan kiwon lafiya guda 100, da tura tawagogin kwararrun kiwon lafiya domin samar da ayyukan jinya. Haka kuma, Sin ta alkawarta ilimantar da 'yan mata, da kuma karbar mata dubu 30 domin tsare-tsaren ba da horo a kasar Sin. Mista Sun Jiwen ya yi furuci ne a gaban wakilan bankin ci gaban Afrika (BAD) dake Gabon, wanda kasar Sin ta zaba a matsayin abokin hulda wajen cimma wasu muhimman ayyukan ci gaba a Afrika. (Maman Ada)