Wani asusun kwararru a fannin gine gine na hadin gwiwar kasar Sin da nahiyar Afirka, ya bayyana burin sa na samar da horon sanin makamar aiki da ake bukata ga matasan Afirka, domin ba da damar samar da dunbin guraben ayyukan yi ga 'yan Afirkan.
A cewar daya daga manyan jami'an asusun Adedana Ashebir, asusun hadin gwiwar Sin da Afirka na SACE, zai kaddamar da sabon shirin na sa a birnin Nairobin kasar Kenya a karshen shekarar 2017 mai zuwa, kafin daga bisani a fadada shirin zuwa sauran kasashen Afirka.
Uwargida Ashebir, ta ce cikin shekarun baya bayan nan, karin kamfanonin kasar Sin na gudanar da manyan ayyukan gine gine a Afirka, kuma fannin na cikin manyan fannoni da ka iya samarwa al'ummar Afirka guraben ayyukan yi masu yawa.
Ta ce, karuwar guraben ayyukan yi na cikin manyan bukatun gwamnatocin nahiyar Afirka, duba da cewa hakan ne kadai zai iya magance illolin dake tattare da fatara da talauci tsakankanin al'umma.
Asusun na SACE dai na ganin kamfanonin Sin suna da babbar gudummawa da za su bayar, wajen zamanantar da fannin gine gine a Afirka, duba da irin ayyukan ci gaba masu yawa da suka riga suka aiwatar a kasar Sin.(Saminu)