Yayin taron, ana saran mahalartansa za su zakulo matakan da za su taimakawa kamfanonin Afirka kara samar da sabbin guraben ayyukan yi da za su kai ga inganta birane da yankunan karkarar kasashen.
Kungiyar tana kuma shirin kaddamar da wani shiri na bunkasa kasashen Afirka, ta hanyar nazarin kwarewar kasashen Afirka ta fuskar raya manufofin da suka shafi masana'antu da yadda za su ci gajiyar manufar ta hanyar yin kwaskwarima da tattauna hanyoyin da za a kara karfin shirin tattalin arzikin Afirka.
Sai dai duk da matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta a sassan duniya, ci gaban nahiyar ta Afirka ya kai kashi 4 cikin 100 a shekarar 2013, idan aka kwatanta da kashi 3 cikin 100 na ci gaban tattalin arzikin duniya.
A wannan shekara dai an yi hasashen ci gaban zai karu zuwa kashi 5 cikin 100 yayin da a shekarar 2015 ci gaban zai tashi daga kashi 5 zuwa kashi 6 cikin 100. (Ibrahim Yaya)