IMF ta ce samun ingancin kudin kasar ta Renmimbi kwarai a wannan shekarar ya maida musanyar kudin a wani matsayin da ba zai sake rage aminci ba.
IMF ta dauki matakin Sin a wannan yunkuri na baya bayan nan da zummar inganta yanayin tsarin musanyar kudi a wani abin maraba domin bada dama ga kasuwanni wajen samu damar taka rawa na tsaida matakin darajar kudin. Haka kuma asusun ta jaddada cewa Sin za ta iya kuma ya kamata ta tunkari wani yanayin musanyar kudi mai karko a cikin shekaru 2 zuwa 3. (Fatimah)