Kamfanonin kasar Sin na COMAC da Avic International da kuma gwamnatin Congo sun rattaba hannu kan wani kundin fahimtar juna na shirin samarwa bangaren Congo jiragen sama, a yayin baje kolin jiragen saman kasa da kasa na birnin Farnborough a kasar Burtaniya da ya gudana daga ranar 14 zuwa 20 ga watan Yuli.
Shugabannin kamfanonin jigaren saman kasar Sin da ministan sufurin kasar Congo, Rodolphe Adada sun cimma wata yarjejeniya kan yiyuwar samar da jiragen sama samfurin ARJ21 ga kasar Congo, in ji wata majiya mai tushe ta kusa da ma'aikatar sufurin kasar Congo.
Zabin wadannan jiragen sama, ya biyon bayan ziyarar da shugaban kasar Congo Denis Sassou N'Guesso ya kawo a nan kasar Sin, a cikin watan Yunin da ya gabata, a albarkacin bikin cikon shekaru hamsin da kulla huldar diplomasiya tsakanin kasashen biyu. (Maman Ada)