Stephen Dujjaric ya ce, mutene fiye da miliyan 5.6 a yanzu haka suna fama da matsakaici ko matsanancin rashin abinci. Inda ya ce kananan yara 'yan kasa da shekaru 5 wadanda wannan lamari ya fi yi ma muni sun wuce adadin wadanda ke cikin bukata na gaggawa da majalissar ta yi kiyasi da tazara mai yawa.
Shirin na WFP na shirin samar da taimakon abinci mai gina jiki ma kusan mutane 600,000 a wani agaji don dakile yunwan da suke fuskanta da rashin matsuguni, in ji Kakakin na MDD. (Fatimah)