Hare haren kunar bakin wake da suka faru a ranar Asabar a kasuwar garin Koulfoua, dake yankin tafkin Chadi, sun yi sanadin mutuwar mutane 19 da ke hade da 'yan kunar bakin wake hudu, tare kuma da raunana mutane 130, a tsibirin tafkin Chadi, a cewar wani adadin wucin gadi da ministan sadarwa na Chadi, kana kakakin gwamnati, Hassan Sylla Bakari ya bayar.
Gwamnati ta aike da ministan kiwon lafiya gami da wata tawagar likitoci zuwa wurin domin bada jinya da daukar nauyin wadanda suka jikkata, yayin da wadanda suka ji rauni mai tsanani za a isar da su zuwa asibitocin da suka tanadi kayan aikin da suka dace, in ji mista Sylla Bakari.
A halin yanzu an samu ciwo kan matsalar, in ji kakakin gwamnatin Chadi tare da yin kira ga al'umma da suka kasance cikin ko ta kwana domin taka birki ga duk wasu ayyukan ta'addanci. (Maman Ada)