Kakakin hukumar 'yan sandan jihar ta Anambra a Nijeriya, Ali Okechukwu ya bayyana cewa, a halin yanzu, rundunar 'yan sanda na gudanar da bincike kan wannan hadari.
Haka kuma, akwai wadanda suka gane ma idanun su da suka bayyana cewa, wata motar dake dauke da tukwanen iskar gas ta fashe a yayin da take sauke su, abin da ya haddasa gobara nan take wanda kuma ya dade yana cin wuta na sa'o'i da dama, abin da da ya haddasa rasuwar wasu ma'aikatan tashar da masu sayen gas, har ma da wasu mutane da suke wucewa wurin a lokacin.
Sai dai a wani labarin kuma da kafofin watsa labaran wurin suka bayar a baya, an ce, mutane sama da dari ne suka rasu sakamakon gobarar da ta tashi a matatar iskan gas din , amma rundunar 'yan sanda ta musa wannan labaran.
Amma wani jami'in wurin da ya boye sunansa ya nuna cewa, ba a iya tabbatar da adadin wadanda suka rasu, mai iyuwa ne, rundunar 'yan sanda ba ta fadi adadin rasuwar mutanen na gaskiya ba. (Maryam)