Masanin Frans Uusiku, wanda babban jami'i ne a hukumar Simonis Storms Securities, ya ce, da farko ya kamata kasashen Afrika su mai da hankali wajen zuba jari a bangaren ilmi da kirkire kirkire, domin hakan zai ba da nahiyar ta Afrika damar yin gogayya da sauran kasashen duniya, musamman wajen sarrafa kayayyaki da hada hadar su. Abu na biyu ya ce, ya kamata dangantakar Sin da Afrika ta mai da hankali wajen shawo kan kalubale a harkar sufuri, musamman wajen samar da muhimman ababan more rayuwa a nahiyar Afrika.
Uusiku ya ce, yunkurin da kasar Sin ta yi na samar da kudi kimanin dalar Amurka biliyan 60 don aiwatar da wasu shirye shirye 10 na tsawon shekaru 3 na dangantakar Sin da Afrika zai yi matukar tasiri mai yawan gaske a Afrika.
Ya ce, wannan aniyar ta yi daidai da shirin kungiyar ci gaban kasashen Afrika na daga martabar nahiyar ta hanyar bunkasa ci gaban tattalin arziki.
A halin yanzu, akwai kalubale masu tarin yawa dake dakile aniyar kasashen Afrikan wajen gudanar da cinikayya a tsakanin su, wadanda suka hada da rashin ingantaccen sufuri, da karancin ababan more rayuwa da rashin ingantaccen tsarin harkokin cinikayya irin na zamani.
Uusiku, ya bukaci kasashen Afrika da su yi kyakkyawan amfani da dandalin FOCAC wajen bunkasa ci gaban harkokin kasuwanci da tattalin arziki, da siyasa da suaran muhimman batutuwa don ci gaban nahiyar. (Ahmad Fagam)