An kaddamar da taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin kananan gwamnatocin Sin da Afirka karo na biyu, wanda kungiyar sada zumunta ta kasar Sin, da kungiyar sada zumunta a tsakanin jama'ar Sin da kasashen Afirka suka dauki nauyin shiryawa.
Taron wanda ya gudana a Talatar nan a birnin Beijing, ya samu halartar mamban majalissar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi, wanda kuma ya gabatar da jawabi.
Cikin jawabin nasa, Yang Jiechi ya bayyana cewa hadin gwiwa tsakanin kananan gwamnatocin kasa da kasa, na da babbar ma'ana ga raya dangantaka tsakanin kasashen duniya. (Zainab)