in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sanya ran cewa taron koli na FOCAC zai jagoranci bunkasuwar dangantaka a tsakanin Sin da Afirka
2015-11-07 13:48:43 cri
A jiya Jumm'a 6 ga wata, shugaban hukumar kula da harkokin kasashen Afirka ta ma'aikatar harkokin waje ta Sin, Lin Songtian ya bayyana a birnin Beijing cewa, yanzu tsarin samun bunkasuwa na Sin da na kasashen Afirka suna dacewa da juna. A don haka, ana sanya ran cewa, taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka wato FOCAC da za a yi a kasar Afirka ta Kudu a wata mai zuwa, zai jagoranci bunkasuwar dangantaka tsakaninsu yadda ya kamata.

A wannan rana, a gun taron manema labaru da hukumar 'yan jarida ta Sin ta shirya, Mista Lin ya bayyana cewa, wannan ne karo na farko da aka shirya taron koli na FOCAC a wata kasar Afirka, hakan na da ma'ana sosai, wanda ya bayyana muhimmancin da Sin ta dora kan nahiyar Afirka.

Mista Lin ya bayyana cewa, kasashen Afirka na fatan raya masana'antu cikin sauri, a yayin da Sin take kokarin kyautata tsarin masana'antunta. Shi ya sa tsarin samun bunkasuwa na bangarorin biyu ya dace da juna sosai. Ya lura da cewa, kasashen Afirka suna da albarkatu da dama, tare da samun mutane masu yawan gaske, yayin da Sin take da kudi da fasahohi da kasashen Afirka suke bukata. A sabo da haka, idan bangarorin biyu suka hada gwiwa tsakaninsu, ba shakka, kasashen Afirka za su sami ci gaba cikin sauri.

Ban da haka, Mista Lin ya kara da cewa, yanzu kasashen Afirka suna fama da rashin manyan kayayyakin amfanin jama'a na zamani, da rashin kwararru. Sin tana fatan taimakawa kasashen Afirka wajen kafa tsarin masana'antu dake iya samun bunkasuwa da kansu, da yin hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka a fannonin aikin gona da na su, a kokarin kafa wani tsarin tabbatar da samar da isasshen hatsi, da yin hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya, a kokarin taimaka masu wajen kafa tsarin shawo kan cututtuka. Bisa wadannan tsare-tsare uku, ana fatan za a warware matsalolin kasashen Afirka uku, wato samar da ayyukan yi, da samun isasshen abinci, da kuma tabbatar da zaman lafiya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China