A cikin wata sanarwar da daraktan ayyukan tsaro a Abuja, Mohammed Mohammed ya fitar, an ce bayanan sirri sun bayyana cewar kungiyar 'yan ta'addan sun kamala shirinsu na kai hari a cikin taron jama'a, musammam mujami'i, masallatai da kasuwanni a cikin kwanaki masu zuwa ta inda za su yi amfani da kananan yara mata wajen aikata kunar bakin waken.
Don haka sanarwar ta bukaci mazauna birnin da su sa ido kwarai su kuma kai rahoton duk wani mutumin da ba su yarda da shi ba.
Kungiyar dai ta Boko Haram yanzu ta dauki salon amfani da yara mata kanana ne wajen kai harin kunar bakin wake a Nigeriya, wanda ya zuwa yanzu mutane kusan 13,000 suka halaka, daruruwa kuma an sace su tun daga lokacin da ta kunno kai a kasar a shekara ta 2009 da zummar son kafa daular islama.
Sojojin Nigeriya sun kwato yawancin yankunan da kungiyar a baya ta karbe a cikin wannan shekarar, amma kuma har yanzu ana ci gaba da kai hari, abin da ke sanadin mutuwar fararen hula da dama.
Shugaban Nigeriya dai Muhammadu Buhari ya ba da karshen watan gobe na Disamba ga sojojin kasar da su kawo karshen ayyukan kungiyar ta Boko Haram. (Fatimah Jibril)