Yawancin jama'a kuma sun samu rauni sakamakon wannan harin da ya faru lokacin da wadannan gungun musulman mabiya wani darika suka taso tun daga Zaria a wani bikin da suke yi zuwa wannan garin mai tazaran kilomita 20 daga cikin birnin kano.
Maharan ya tayar da bam din dake jikin shi ne a tsakiyar wadannan mutane bayan da ya yi badda kama ya saje a cikin masu bikin, in ji wani jami'in tsaro da ya nemi a sakaya sunan shi.
Wani jami'in a wannan gari ya ce, za'a bayyana adadin wadanda suka mutu ga manema labarai bayan an kamala ba da aikin ceto.
Ana dai zargin kungiyar Boko Haram ne da kai wannan hari wadda take yi a arewacin Nigeriya a kokarin kafa daular Islama. (Fatimah Jibril)