Shugaban Chadi Idriss Deby Itno, ya sanya hannu a ranar 9 ga watan Nuwamban shekarar 2015, ga dokar ta baci a wannan yankin mai iyaka da kasashen Kamaru, Nijar da Najeriya da ya kasance wata mashiga da wata mahadar kungiyar Boko Haram.
Matakin sanya dokar ta bacin na baiwa gwamnan yankin tafkin Chadi ikon hada zirga zirgar jama'a, kebe yankuna bada kariya ko tsaro, takaita rangadin mutane, bada umurnin gudanar da bincike a gidaje da dare ko da rana bisa umurnin babban alkalin kasa, da kuma karbe makamai daga hannun mutane da sauransu.
Gwamnatin Chadi ta dauki niyyar rakiyar wannan dokar ta bacin tare da wasu ayyukan cigaba jama'a da na tattalin arziki, a fannonin noma, kiwo, ilimi da kiwon lafiya. Inda gwamnatin kasar ta kebe Sefa biliyan 3 domin wannan shiri na cigaban jama'a da tattalin arziki.
Idan sojojin Chadi dake a kasar Kamaru da Najeriya, sun taimaka wajen rage karfin Boko Haram sosai, to wannan kuma ya janyo ma Chadi bakin jini, da fama da hare haren Boko Haram da suka shafi babban birnin kasar da yankin tafkin Chadi sau da dama tun daga ranar 15 ga watan Junin shekarar 2015. (Maman Ada)