Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya fadawa manema labarai a Litinin din nan cewar, bayan raba mutanen da gidajensu, har ila yau, kimanin makarantu dubu da 100 ne mayakan na Boko Haram suka lalata a yankin tafkin Chadi cikin shekarar nan.
Dujarric, ya tabbatar da hakan ne bayan samun kiddigar daga Toby Lanzer, jami'in MDD a sashen taimakon jin kai a yankin Sahel.
A cewar Lanzer, a yankin na Sahel, kusan mutane miliyan 25 ne ke fama da matsalar karancin abinci, yayin da matsalar tafi kamari kan mutane miliyan 5. Ya kara da cewa, kimanin kananan yara dubu 700 ne ke mutuwa a duk shekara a yankin a sakamakon matsalar karancin abinci mai gina jiki.
Lanzer wanda ya kasance jami'in MDD a jamhuriyar tsakiyar Afrika daga wata Yuli, ya ce, mayakan na Boko Haram sun kaddamar da hare hare a makarantun kasashe 4 da suka hada da jamhuriyar Kamaru, da jamhuriyar Nijer da kuma tarayyar Najeriya. (Ahmad Fagam)