Sanarwar ta kuma bayyana kudurin shugabannin na cimma nasarar bunkasa kasashen dake yankin Asiya da Fasifik, cikin kyakkyawan yanayi da wadata, ta yadda kasashen za su samu ci gaba mai dorewa a fannonin tattalin arziki da fannin kere-kere. A jiya Laraba ne dai aka bude taron tattalin arzikin na APEC, aka kuma kammala a yau Alhamis, yayin da kuma ake sa ran gudanar da na shekara mai zuwa a kasar Peru.