Taron mai taken gina tattalin arziki don samar da kyakkyawar duniyar da muke ciki, zai mayar da hankali ne kan wasu fannoni guda 4, na farko shi ne hade tattalin arzikin shiyyar waje guda, habaka kanana da matsakaitan masana'antu, shiga harkokin kasuwannin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, zuba jari a bangaren inganta rayuwar jama'a da kuma gina al'umma mai wadata.
Ana saran yayin taron na kwanaki biyu shugaba Xi zai bayyana manufofin kasar Sin game da hadin gwiwar kasar Sin a yankin Asiya da Fasifik, sannan ya yiwa sauran shugannin da ke halartar taron bayani game da yadda aka aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma yayin taron kolin kungiyar da ya gudana a birnin Bejing a shekarar da ta gabata.
Bugu da kari, ana saran shugaba Xi zai zayyana ci gaban da aka samu game da shirin nan na Ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar da kuma irin damammakin da shirin ya samarwa shiyyar.
Tun da farko dai shugaba Xi ya gabatar da jawabi a taron shugabanni a fannin masana'antu da cinikayya na APEC. (Ibrahim)