A yayin ganawar tasu, Yang ya bayyana cewa, a matsayinta na wata muhimmiyar hukumar masana masu kaifin basira, South Center ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa, da karfafa hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa da na masu ci gaba. Ya ce kasar Sin na fatan kara hadin gwiwa da South Center, don taimakawa kasashe masu tasowa wajen tabbatar da samun bunkasuwa da wadata tare.
A nasa bangare Mkapa ya bayyana cewa, hukumarsa na fatan ci gaba da kokari tare da kasar Sin, a fannin zurfafa hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa, da ba da gudummawa kan tabbatar da ajandar samun dauwamammen ci gaba na shekarar 2030. (Bilkisu)