in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta zamo daya daga jagoran kungiyar G20
2014-12-13 17:27:38 cri
Mataimakin ministan kudin kasar Sin Zhu Guangyao, ya ce a matsayin kasar da za ta karbi bakuncin taron koli na kungiyar G20 a shekarar 2016, tun daga yanzu ne Sin ta hada kanta da kasashen Turkiya da Australia a matsayinsu na jagoran kungiyar, don su ci gaba da sa kaimi ga aikin kwaskwarima ga tsarin kulawa da tattalin arzikin duniya, da bada gudummawa ga bunkasa tattalin arzikin duniya.

Mr. Zhu wanda ya bayyana hakan a jiya Jumma'a, bayan da ya halarci taron mataimakan ministocin kudi, da na shugabannin manyan bankunan kasashen kungiyar G20 da ya gudana a birnin Istanbul na kasar Turkiya, ya bayyana wa 'yan jarida cewa, kasar Australia ce ta jagoranci kungiyar G20 a bana, yayin da Turkiya za ta jagoranci kungiyar a badi, sai kuma kasar Sin da za ta jagoranci G20n a shekarar 2016.

A sabili da haka ne a cewarsa, kasashen uku, za su taka muhimmiyar rawa, wajen tsara ayyukan kungiyar, wadanda zasu kyautata tsarin ta, da kuma sa kaimi ga dauwamammen ci gaban tattalin arzikin duniya.

Ya yin taron na yini 2, wakilai mahalarta sun nuna sha'awarsu ga tsarin tattalin arzikin Sin. Game da hakan Mr. Zhu ya ce tattalin arzikin Sin yana bunkasa cikin sauri, yana kuma sahun gaba a duniya baki daya. Ya ce a bana, Sin ta ba da gudummawa mai yawa ga bunkasa tattalin arzikin duniya, da kason da ya kai 27.8 cikin dari, yayin da Amurka ta ba da gudummawar kaso 15.3 cikin dari. Wanda hakan ke nuna cewa kasashen Sin da Amurka, sune kan gaba wajen bada gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China