A gun taron, an bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, yawan hatsi da ake samu ya rika karuwa, ya zama dole a noma hatsi da yawa a lokacin zafi na bana. Ko da ya ke babu isasshen wurin ajiye su a wasu wurare. A sabili da haka, adana amfanin gona yadda ya kamata na da muhimmanci kwarai a yanzu, har ma a cikin dogon lokaci mai zuwa. Dole ne a dauki matakai iri iri, domin kara karfin adana hatsi da kafa dakunan adana abinci, a kokarin tabbatar da cewa, ba a rasa abinci kwata-kwata ba.(Fatima)