Ana sa ran a lokacin ziyarar, firaministan na Sin Li Keqiang zai gana da shugabar kasar Koriyan ta Kudu Madam Park Geun-hye da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar, sannan ya halarci ayyukan hadin gwiwwa kan tattalin arziki da na musanyar al'ummomi.
A lokacin taron tattaunawa tsakanin Sin, Japan da Koriya ta Kudu da za'a yi bayan tsaikon shekaru uku da rabi, ana sa ran shugabannin kasashen uku su yi musanyar ra'ayi kan hadin gwiwwa da kuma batutuwan da suke jawo hankalin yankunansu da ma sauran duniya baki daya. Haka kuma za su halarci taron tattaunawa na kasuwanci. (Fatimah Jibril)