Zhu Min ya bayyana wa 'yan jarida a yayin taro na uku kan batun tattara kudi da samun bunkasuwa na MDD da ya gudana a birnin Addis Ababa cewa, kasar Sin muhimmiyar mamba ce a asusun na IMF, kuma tana da hannun jari a IMF, kana ta kara samar da rancen kudi ga IMF don taimakawa sauran kasashe masu tasowa, musamman kasashe masu fama da talauci. A matsayinta na kasa mai tasowa, Sin ta taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.
Zhu Min ya ce, kasar Sin tana goyon bayan asusun IMF ya samar da gudummawa ga kasashe masu tasowa a fannin fasahohi.
An gudanar da taro na uku kan batun tattara kudi don gudanar ayyuka ci gaba na MDD ne daga ranar 13 zuwa 16 ga wata a birnin Addis Ababa. Za kuma a yi kokarin cimma ajandar gudanar da ayyuka ta Addis Ababa wadda za ta nuna goyon baya ga samun bunkasuwa mai dorewa a duniya a shekaru 15 masu zuwa, wannan yana daga cikin abin da za a mayar da hankali kansa a taron koli kan batun samun bunkasuwa da za a gudanar a cibiyar MDD a watan Satumba na bana, da kuma taron yanayi na MDD da za a gudanar a birnin Paris na Faransa a watan Disamba na bana. (Zainab)