Kasar Somaliya ta kaddamar da wani dandalin tuntuba wanda zai tattauna shirye-shiryen gudanar da zabukan da za a gudanar a kasar a shekarar 2016.
Wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar a karshen taron, ta bayyana cewa, dandalin wanda ya kunshi wakilan gwamnati, shiyyoyin jihohin kasar, kungiyoyin fararen hula da abokan huldar kasa da kasa, zai yi ganawarsa ta farko a ranar 14 ga watan Oktoba don tsara jadawalin zabukan kasar.
Wakilin musamman na babban sakataren MDD a kasar Somaliya Nicholas Kay ya bayyana cewa, dandalin na da muhimmancin gaske ga shirin wanzar da zaman lafiya a kasar. Kana zai jagoranci shirin mika mulki ga zababbiyar gwamnati yayin da wa'adin gwamnati da na 'yan majalisar kasar ya kare a shekara mai zuwa.(Ibrahim)