Faraministan kasar Somaliya Abdiwelish Ahmed Mohamed ya jaddada a ranar Laraba a birnin Bujumbura, hedkwatar kasar Burundi, yiyuwar kasarsa ta gudanar da zabubukan shekarar 2016.
Da yake ziyarar aiki a kasar Burundi, Ahmed Mohamed ya samu ganawa tare da shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza, tare da gabatar masa godiyar gwamnatin Somaliya bisa ga tura sojojin Burundi kusan dubu shida a kasar Somaliya a cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta tarayyar Afrika a Somaliya (AMISOM). Firaministan Somaliya ya shaidawa shugaban kasar Burundi cewa, mayakan kungiyar Al-Shabaab ba su da wata hedkwata a yanzu, kana kuma kasarsa na shirin gudanar da zabubuka a shekarar 2016.
Dakarun AMISOM sun karbe wasu biranen da mayakan Al-Shabaab suka mamaye a baya, in ji mista Mohamed.
Rukunin sojojin Burundi na gudanar da aiki mai kyau, kuma 'yan kasar Somaliya na yabawa da aikin kasar Burundi da ma na gamayyar kasa da kasa, in ji Gervais Abayeho, kakakin shugaban kasar Somaliya a gaban 'yan jarida bayan ganawar shugabannin biyu. (Maman Ada)