Mahukuntan kasar Somaliya sun kaddamar da sabbin manufofin inganta tsaron kasa, a wani mataki na tabbatar da nasarar wanzar da zaman lafiya a fadin kasar.
Cikin wata sanarwa da ya fitar game da hakan, shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud ya ce, ya zama dole a dauki matakan sake ginin kasar, da hada kan al'ummunta, da kuma tabbatar da gudanar da manufofin tsaron kasa a fayyace.
Shugaba Mohamud ya kara da cewa, gwamnatinsa ta samu nasarar kwato sassan kasar masu yawa, wadanda a baya mayakan Al-Shabaab suka mamaye.
Sabbin manufofin da gwamnatin kasar Somaliya ke nufin aiwatarwa a bangaren inganta tsaro, sun hada da baiwa jami'an tsaro hakkokinsu yadda ya kamata, da tantance yawan jami'an tsaron, aikin da ake sa ran gayyatar wakilan kasashen ketare domin gudanar da shi cikin watanni uku masu zuwa. Sauran fannonin da ake fatan ingantawa, sun hada da gudanar da gyaran fuska a sashen kashe kudaden tsaro, da baiwa sauran kasashen duniya damar shiga aikin tabbatar da tsaron kasar.
Yanzu haka dai gwamnatin Somaliya, wadda ke samun goyon bayan kasashen duniya a yakin da take yi da dakarun kungiyar Al-Shabaab, na shan fama da hare-haren mayakan kungiyar a ciki da wajen kasar. (Saminu)