A yayin ganawarsa tare da shugaba Boni Yayi, da farko ya yi wa Boni Yayi godiya kan yadda ya kula da huldar dangantaka tsakanin kasashen biyu, da kuma kokarinsa wajen ganin an maido da huldar dangantaka. Mista Van Dyck Joseph ya tabbatar masa da nasa goyon baya, wajen maido da dangantaka har ma da kulawa da ita yadda ya kamata, in ji mista Joannes Joseph.
Netherland da Benin sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aiwatar da tsarin tallafawa bangaren samar da ruwa da tsaftace muhalli (PPEA-II) kashi na biyu bisa kudin Sefa biliyan 40,524 a tsawon lokacin shekarar 2013 zuwa shekarar 2015.
Wannan tsari na da nufin tabbatar da samar da ruwa sha ga al'ummomin kasar Benin, magance hadarukan dake da nasaba ga kulawa da ruwa da bada taimako wajen bunkasa aikin kula da tsaftar jiki da tsaftace muhalli tun daga tushe. (Maman Ada)