Wakilan gwamanatocin Sin da na Benin sun kulla wani shirin hada kai ta fuskar al'adu na shekarar 2014 zuwa 2017 a birnin Cotonou, hedkwatar kasar Benin, shirin da ke da burin bunkasa zumunta tsakanin jama'ar kasashen biyu.
An gudanar da wannan biki ne dai a dakin taro na ma'aikatar al'adun kasar.
A madadin kasashen biyu, jakadan kasar Sin dake kasar Benin Tao Weiguang, da minista mai kula da harkokin al'adu, yaki da jahilci, da sha'anin hada kayayyaki da yawon shakatawa na kasar Benin Jean-Michel Abimbola ne suka sanya hannu kan takardar amincewa da shirin.
Minista Abimbola ya yi amfani da wannan dama wajen godewa matakin da Sin ta dauka, na sanya Benin matsayin farko daga jerin kasashen da ta kafa cibiyar al'adun ta, yana mai alkawarta ci gaba da goyon bayan bunkasuwar wannan cibiya. (Amina)