Yarjejeniyar bada rancen kudin kan shirin sadarwa bisa dogon zango, an rattaba hannun kanta a ranar Litinin a birnin Cotonou tsakanin ministan harkokin wajen kasar Benin da dunkulewar Afrika, forfesa Nassirou Arifari Bako da jakadan kasar Sin dake kasar Benin, Diao Mingsheng.
Miao Mingsheng ya ce, ganin cewa gwamnatin Benin na sanya muhimmanci sosai kan gina ababen more rayuwa na sadarwa, don haka yana fatan wannan shirin zai baiwa dukkannin al'ummar kasa Benin damar yin amfani da internet, layin internet mai inganci da zai saukakawa kowa zaman rayuwa. Haka kuma yana fatan bangarorin biyu zasu aiki tare domin cimma wannan shirin cikin gajeren lokaci. Ya kara da cewa, internet na taimakawa ci gaban tattalin arziki da jama'a, kana sanya hannu kan wannan yarjejeniya wata babbar dama ce ta karfafa huldar dangantaka tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Benin, ya bayyana cewa ta hanyar sanya hannu kan wannan yarjejeniya, gwamnatin kasar Sin ta kara nuna niyyarta ta tallafawa kasar Benin cikin sahihanci da gaskiya kan kokarin da kasar na yau da kullum domin samun ci gaba. (Maman Ada)