Masu fashin baki a fannin tattalin arziki a Najeriya, sun yi hasashen cewa, kasar za ta yi matukar amfana, daga tallafin dalar Amurka biliyan 2.1, wanda babban bankin duniya ya alkawarta samarwa domin sake ginin yankunan arewa maso gabashin kasar.
Bankin duniyar dai ya alkawarta baiwa Najeriya wannan tallafi ne a matsayin rance mai rangwame, yayin tattaunawar shugaban bankin da kuma shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, a ranar Talatar da ta gabata a birnin Washington.
Game da hakan, wasu masana a fannin tattalin arziki dake jihar Legas a kudancin Najeriya sun bayyana cewa, matakin ya dace da bukatar da ake da ita, ta sake farfado da yankunan wadanda rikicin Boko Haram ya lahanta.
Da yake tsokaci game da lamarin, daya daga masanan Osi Itsede, ya ce, samun wannan rance alama ce dake nuna kwazon gwamnatin Najeriya a fannin farfado da tattalin arziki da zamantakewar al'ummar wannan yanki.
Ya ce, bisa tsarin samar da rancen, Najeriya za ta gabatar da shirinta na sake ginin yankunan, wanda za a aiwatar da hadin gwiwar shirin babban bankin duniyar na samar da ci gaba.
A nasa bangare Mr. Titus Okurounmu, tsohon darektan babban bankin Najeriya, cewa ya yi, gwamnatin Najeriyar za ta iya amfani da kudaden rancen wajen samun riba, idan an samar da su kafin murkushe ayyukan tada kayar baya a yankunan na arewa maso gabashi. Ya kuma yi fatan kudaden za su ba da damar tsara shirye-shirye, wadanda za su kara janyo hankulan masu zuba jari na kasa da kasa. (Saminu)