A gun bikin sa hannu kan yarjejeniyar, jakadan Sin dake kasar Kenya Liu Xianfa ya bayyana fatan kasar Sin ga kasar Kenya, wato tana fatan gudummawar tantuna da ta samar wa 'yan gudun hijira na kasar Somaliya dake kasar Kenya za ta sassauta matsalar karancin kayayyaki a sansanin Daadab, da taimakawa wajen tsugunar da 'yan gudun hijira na Somaliya. Sa'an nan, hadin gwiwar fasahohi game da cibiyar wasanni ta Moi zai taimaka wa kasar wajen horar da 'yan wasa matasa da daukar bakuncin manyan gasannin kasa da kasa. Kuma gina babban ginin kwalejin Confucius a birnin Nairobi zai samar da yanayi mai kyau ga matasan kasar Kenya wajen koyon harshen Sinanci da ma al'adun Sin.
Ministan kudi na kasar Kenya Henry Rotich ya nuna godiya ga kasar Sin bisa wannan gudummawar da ta samar. Ya ce, daddale yarjejeniyar a wannan karo na shaida ingancin dangantakar dake tsakanin gwamnatoci da jama'ar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)