Zhou ya bayyana bakin cikinsa game da yadda ake aiwatar da shirin yin gyare gyare kan rabon IMF, kuma ya ce kamata ya yi bangarori daban daban su yi iyakacin kokarinsu domin kiyaye amanar asusun IMF.
Darektocin gudanarwa na asusun IMF sun cimma matsaya kan shirye-shiryen yin kwaskwarima ga kason kasashe daban daban cikin asusun da aikin kulawa da asusun a watan Nuwamba na shekarar 2010. Bisa wannan shiri, matsayin Sin za ta canza daga na shida zuwa na uku bisa kasonta, yayin da yawan kason kasashe masu sukuni zai ragu zuwa kashi 57.7 cikin dari, sannan yawan kason kasashe masu tasowa zai karu zuwa kashi 42.3 cikin dari. Amma har zuwa yanzu ba a sami ainihin ci gaban gudanar da wannan shiri ba sabo da rashin amincewar Amurka, wanda kuma zai kasance muhimmin shirin yin kwaskwarima ga asusun IMF a cikin tarihinsa na tsawon shekaru 65.
An gudanar da taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankuna na G20 a birnin Washington daga ranakun 16 zuwa 17 ga wata. A yau Lahadi ne kuma babban bankin kasar Sin ya gabatar da wasu batutuwa dangane da wannan taro.(Fatima)