A yayin ganawar tasu a jiya Litinin, Li Keqiang ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen duniya su karfafa shawarwarin dake tsakaninsu kan manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, domin tabbatar da zaman karko a sha'anin kudin duniya, da kuma samar da yanayi mai kyau da zai dace da farfadowar tattalin arzikin duniya.
Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a tsarin tattalin arzikinta, da kuma kwaskwarima a sha'anin kudi, domin raya tattalin arziki da kuma kandagarkin matsalar kudi, ta yadda za a nuna goyon baya da ba da taimako wajen kafuwar kamfanoni, da kirkire-kirkire yadda ya kamata.
A nata bangare, Christine Lagarde ta bayyana cewa, nasarar yin kwaskwarima kan sha'anin kudin da kasar Sin ta cimma, za ta kasance abin koyi ga sauran kasashen duniya, kana za ta ba da taimako game da tabbatar da zaman karko a sha'anin kudin duniya. (Maryam)