A ranar Alhamis din nan 11 ga wata MDD ta yi kira ga kasashen Afrika da su inganta ayyukan kwadagonsu domin a rage yawan talauci a yankin.
Babban sakatare a ofishin taro a kan ciniki da cigaba Mukhisa Kituyi wanda ya shaida wa manema labarai hakan a Nairobin Kenya ya ce, tsarin janyo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje ta hanyar albashi kadan ba wanda zai tafiyar da ayyuka na tsawon lokaci ba ne.
Mr. Kituyi, lokacin da yake magana a wajen kaddamar da rahoton ofishin game da ciniki da cigaba na shekarar 2014, ya lura da cewar, ayyukan da suke da karfin ma'aikata za su tabbatar da cewa, Afrikan ta samar da ababe masu aminci da za su iya takara da kasuwannin kasashen waje.
Ya ce, nahiyar tana da albarkatun kasa da za su iya ingiza samar da masana'antu, abin da kawai ya rage shi ne yadda za'a samar da tsarin mai kyau na yin hakan wanda zai sa nahiyar ta zama babbar cibiyar samar da kayayyaki masu inganci da kuma fitar da su zuwa kasashen duniya.
Ya ce, a yanzu haka kasashen Afrika da dama sun dogara ne a kan fitar da kayayyaki masu araha a matsayin babban cigaban tattalin arzikinsu.
A cewar ofishin UNCTAD, duniya gaba daya tana kauracewa dogaro a kan kayayyakin da ake samar da su domin fitarwa waje kadai, a janyo hankalin masu zuba jari kai tsaye saboda za su biya kudin kwadago kadan ba zai taimaki nahiyar wajen cimma matsayin samun kudin da ya kamata ba.
Ya lura da cewa, zuba a bangaren ababen more rayuwa zai samar da albarkatun kasa da za'a sayar a kasuwanni kai tsaye, don haka ya bukaci nahiyar ta Afrika da ta yi koyi da kasar Sin game da yadda ta samu nasarar tsallake rikicin tattalin arzikin duniya da ya auku ta hanyar habaka kasuwanninta na cikin gida. (Fatimah)