Wani hasashe da kwamitin tsara manufofin kudi na yammacin nahiyar Afirka MPC ya fitar, ya nuna cewa, kasashen nan takwas dake amfani da kudin Franc, na iya samun koma bayan tattalin arziki, ta yadda a shekarar 2014 mai zuwa ba za su iya cimma kaso 7.3 bisa dari na ci gaban da a baya aka yi musu hasashen samu ba.
Wata sanarwa da kwamitin ya fitar ranar Alhamis 5 ga wata a Dakar, babban birnin kasar Senegal, ta bayyana cewa, kasashen 8 dake karkashin kungiyar UEMOA, wato Benin, da Burkina Faso, da Cote d'Ivoire, da Guinea Bissau, da Mali, da Niger, da Senegal da kuma Togo, na fuskantar koma baya ne sakamakon halin rashin tabbas, da tsaiko a fannin ci gaba da kasashe masu tasowa ke fuskanta.
Har ila yau sanarwar ta ce, karancin riba kan hajojin da kasashen ke fitarwa kasuwannin waje na cikin dalilan wannan matsala, don haka ne ma MPC ta rage makin manyan bankunan wadannan kasashe zuwa 25.
Duk da wannan hasashe na koma baya, a hannu guda MPC ya yi amanar cewa, za a samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki, sakamakon karyewar farashen hatsi, da faduwar farashin danyan mai a wasu daga kasashe mambobin kungiyar ta UEMOA, hakan kuwa, a cewar waccan sanarwa, ba ya rasa nasaba da saukar da farashin danyan mai a manyan kasuwannin duniya ke yi. (Saminu)