Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU tare da MDD gaba daya sun dau alkawarin nuna hadin kansu domin karfafa hadin gwiwwa da kasashen dake yankin tabkuna.
Madam Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar kungiyar AU ta sanar da hakan a ranar Talatan nan lokacin da ta gana da sabon manzon musamman na MDD a yankin tabkunan nahiyar, Said Djinnit a cibiyar kungiyar dake birnin Adis Ababa na kasar Habasha, kamar yadda sanarwa daga kungiyar ta bayyana.
Said Djinnit ya kuma tattauna da kwamishinan kungiyar a bangaren zaman lafiya da tsaro Smail Chergui, wanda a lokacin tattaunawar suka mai da hankali a kan hanyar da za a samar da taimako ga kokarin sauran kasashen duniya a wannan shiyyar domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da hadin gwiwwa a jamhuriyar demokradiyar Kongo, da ma yankin baki daya domin a samu nasarorin da aka gani cikin 'yan watannin nan ya inganta.
Hukumomin biyu sun jaddada bukatar da ke akwai ta inganta tare da karfafa tabbacin a tsakanin kasashe na wannan yankin, a kammala ayyukan wargaza duk wassu rundunar masu dauke da makamai ba bisa ka'ida ba, a mai da hankali yadda ya kamata a kan tattalin arziki da ci gaba a wannan tsari da ake son cimmawa na zaman lafiya, tsaro da hadin gwiwwa. (Fatimah)