in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kiwon lafiya na duniya karo na 68 a Geneva
2015-05-19 16:01:59 cri

A jiya ne aka bude taron kiwon lafiya na duniya karo na 68 a birnin Geneva, inda wakilai daga kasashe membobin hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO 194 suka halarci taron, ciki har da shugabar tawagar kasar Sin kuma direktar hukumar kiwon lafiya da kayyade haihuwa ta Sin Madam Li Bin.

Taron kiwon lafiya na duniya muhimmin taron shekara-shekara ne da hukumar WHO ke shiryawa. Kana shekarar bana shekara ce ta karshe ta cimma burin bunkasuwa na shekarar 2000 na MDD, don haka taron a wannan karo yana da babbar ma'ana. Babbar direktar hukumar lafiya ta duniya WHO Margaret Chan ta yi nuni a cikin rahoton aikin da ta gabatar cewa, yanzu hukumar lafiya ta duniya WHO tana yiwa tsare-tsarenta kwaskwarima, musamman tun lokacin da aka samu barkewar cutar Ebola a shekarar da ta gabata, wadda ta kasance kalubalen da kasashen duniya suka fuskanta a fannin kiwon lafiya. Madam Chan ta bayyana cewa,

"Kasashen duniya ba su shirya sosai don tinkarar cutar Ebola ba. An samu barkewar cutar Ebola mai tsanani a wannan karo wadda ta dade tana shafar kasashe da dama, lamarin da ya sa hukumar lafiya ta duniya WHO ta gamu da matsala wajen tunkarar matsalar . An kuma bukaci hukumar WHO da ta kara mayar da hankali wajen tinkarar matsalar, wadda ba a taba gamuwa da ita ba a tarihin hukumar na shekaru kimanin 70."

Madam Chan ta bayyana cewa, barkewar cutar Ebola ta sa kaimi ga hukumar WHO wajen gaggauta yin kwaskwarima, kuma muhimmin aikin dake gaban hukumar shi ne bullo da shirin ko-ta-kwana na tinkarar duk wata matsala da ta bayyana a fadin duniya. Don haka, Madam Chan ta gabatar da shirin yin kwaskwarima, ciki har da tsara shirin tinkarar matsala a fannin kiwon lafiya cikin gaggawa da babbar direktar hukumar WHO ta bada jagoranci kai tsaye, da kafa wani rukunin tinkarar batun kiwon lafiya a fadin duniya, da tsara sabbin matakai don tinkarar matsala cikin sauri, da kuma kebe kudi na kimanin dala miliyan 100 don tinkarar abin da ya faru kwatsam, da dai sauransu. Chan ta bayyana cewa, za ta kammala dukkan ayyukan da ta gabatar kafin karshen shekarar bana. Ta ce,

"Wannan sabon shiri ya maida hankali kan daukar matakai wajen warware matsala cikin sauri.Kuma ni zan dauki nauyin wannan shiri kai tsaye, kana zan jagoranci membobin hukumar wajen gudanar da shirin. Za a tabbatar da ayyukan da za a gudanar kamar yadda aka tsara, alal misali, ana kayyade ayyukan da za a yi a cikin sa'o'i 24, ko 48 ko 72, bayan barkewar wata annoba, ba matakin na dogon lokaci kamar watanni ba."

Don haka, taken taron kiwon lafiya na duniya a wannan karo shi ne bullo da tsarin kiwon lafiya don tinkarar duk wata matsalar da ta kunno kai. A gun muhawarar da aka gudanar a wannan rana, wakilai masu halartar taron sun bayyana ra'ayoyinsu game da taken taron. Direktar hukumar kiwon lafiya da kayyade haihuwa ta Sin Madam Li Bin ta yi bayani game da yanayin bullo da tsarin kiwon lafiya don tinkarar matsala bisa ka'idojin kiwon lafiya na duniya, da matakan Sin na taimakawa kasashen yammacin Afirka wajen tinkarar cutar Ebola ta hanyar samar da kudade da tura likitoci. Li Bin ta bayyana cewa, ana bukatar yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya wajen bullo da tsarin kiwon lafiya don tinkarar duk wata irin matsala. Li Bin ta ce,

"Gwamnatin Sin tana goyon bayan matakin hukumar lafiya ta duniya WHO na bullo da wani tsarin tinkarar matsalar kiwon lafiya a duniya, da rukunin tinkarar matsalar, da kuma asusun da ake shirin kafawa a wannan fanni. Wannan wani muhimmin mataki ne wajen bullo da tsarin kiwon lafiya na tinkarar duk wata irin matsala, kasar Sin a shirye ta ke ta amsa kiran shiga ayyukan da aka yi a duk lokacin da aka samu barkewar matsalar kiwon lafiya ba zato ba tsammani a fadin duniya." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China