in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta nanata goyon bayanta ga sashin kiwon lafiya a Afirka
2013-05-07 12:50:41 cri






Kasar Sin ta nanata kudurinta a fuskar tallafawa Afirka ta bunkasa sashin kiwon lafiya sakamakon dinbin kalubale da nahiyar take fuskanta, ta hanyar kara zurfafa hadin gwiwa a fannin lafiya.

A cikin wata wasika da aka gabatar yayin zaman tattaunawa na kasa da kasa jiko na hudu kan hadin gwiwar kasar Sin da nahiyar Afirka a fuskar lafiya, mataimakin ministan hukumar lafiya da tsara iyali na kasar Sin Ma Xiaowei ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi musaya da Afirka, na ci gaba da ta samu a fuskar kiwon lafiya da kuma ba da goyon baya ga dabarun Afirka a fannin kiwon lafiya.Ya ce, "Ya kamata a kyautata hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a dukkan fannonin kiwon lafiya. A shirye muke mu yi aiki da Afirka a fuskar bunkasa hadin gwiwa tsakaninmu, karkashin tsarin wannan dandali, domin ta zamo wata muhimmiyar aba ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka."

Ma ya ci gaba da cewa, Sin a shirye take ta yi aiki da gwamnatocin Afirka da ma kafofi masu zaman kansu, kana za ta hada kai da dukkan masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya. Yana cewa, "Muna kuma fatan ganin cewa, an samu karin cibiyoyin kiwon lafiya, masu harkar bincike, jami'o'i, da kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Sin suna kara mai da hankali da kuma kara shiga nahiyar Afirka don ba da karin gudummawa ga hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kiwon lafiya."

Bugu da kari, Ma Xiaowei ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki kut da kut da kasashen Afirka, a kan ayyukan hadin gwiwa na hukumar lafiya ta duniya, WHO da sauran hukumomin kasa da kasa domin a samun ganin cewa, ana amfani da albarkatun kiwon lafiya cikin daidaito, kana Sin da Afirka su iya shawo kan kalubale na kiwon lafiya tare, a karkashin sabon yanayi. Ya ce, "Za mu kara sa himma kan kokarin hukumar lafiya ta duniya, da na MDD, UNAIDS, da ma sauran kungiyoyin kasa da kasa, kana za mu ba da goyon baya ga sabbin matakai da dabaru don bunkasa kiwon lafiya a Afirka."

A nasa bangare, ministan lafiya na kasar Botswana, John Seakgosing cikin bayaninsa yayin bukin kaddamarwan, ya ce, tun lokacin da aka bullo da wannan zaman tattaunawa kan hadin gwiwar kiwon lafiya tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2009, an samu karin damar yin shawarwari da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Ya ci gaba da cewa, "Wannan zaman shawarwari tsakanin Sin da Afirka dangane da hadin gwiwa a fuskar kiwon lafiya wata alama ce dake nuna dagewar kasar Sin a fannin tallafawa Afirka."

Ya kara da cewa, wannan shi ne karo na farko da aka yi zaman shawawarin a Afirka, kuma karo na farko da masu zaman kansu a fannin kiwon lafiya daga Sin da Afirka za su samu damar haduwa da juna da kuma kafa dangantaka wadanda za su kai ga haifar da samun hadin gwiwa nan gaba. Ya ce, "Wannan abin farin ciki ne, domin kamar yadda muka sani, sassa masu zaman kansu suna taka muhimmiyar rawa".

Sin da Afirka sun jima da kafa hadin gwiwa a fuskar kiwon lafiya. Tun daga lokaci da kasar Sin ta tura tawagar farko ta kiwon lafiya zuwa Afirka a shekarar 1963, Sin ta yi amfani da dukkan wata kafa, wajen taimakawa Afirka a fuskar kiwon lafiya ta hanyar gina cibiyoyin kiwon lafiya, samar da magunguna da na'urori, shirya taron kara ilmi ma Afirka da kuma daukar nauyin karatu, duka da nufin gina kiwon lafiya ta hanyar kwarewa da karin fasaha a nahiyar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China